Tankiya kan bashin Amurka na kara zafi

Shugaba Obama na Amurka Hakkin mallakar hoto b
Image caption Shugaba Obama na Amurka

Yayinda wa'adin warware matsalar bashin Amurka ya rage saura kwanaki uku, batun ya sake komawa zauren majalisar wakilai, da kuma majalisar dattawa.

Dukkan majalisun na son ganin an kada kuri'a kan shirin da jam'iyyar Democrat ke mara wa baya na kara yawan kudaden da Amurkar zata iya karba bashi zuwa dala trillion goma sha hudu, matakin da zai sa gwamnatin Amurkar kauce ma zama mai taurin bashi.

Tun da farko shugaba Obama ya yi kira ga bangarorin biyu da su cinma matsaya.

Kafin haka dai majalisar wakilai ta amince da wani shiri da 'yan jam'iyyar Republican ke goya wa baya.