Gaddafi ya yi tsokaci kan mutuwar kwamandan 'yan tawaye

Image caption Kanal Gaddafi

Gwamnatin Kanar Gaddafi ta ce kisan da aka yi wa kwamandan sojojin 'yan tawayen kasar wata alama ce da ke nuna cewa 'yan tawayen ba za su iya tafiyar da al'amura a kasar ba.

Wani kakakin gwamnati ya soki matakin da Burtaniya ta dauka na amincewa da majalisar 'yan tawayen a matsayin wadanda ke da iko a Libya, inda ya ce 'yan tawayen sun kasa iya kare shugabannin su.

An harbe janaral Yunus har lahira ne a ranar Alhamis a wani yanayi mai daure kai.

A halin da ake ciki rahotanni sun ce an ji fashewar wadansu abubuwa da safiyar yau Asabar a wani waje da ke kusa da harabar gidan kanar Gaddafi a birnin Tripoli.