Anders Breivik na da niyyar kai karin hare-hare a Norway

Anders Breivik Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Anders Breivik

Jami'an 'yan sanda a kasar norway sun tabbatar da cewa, Anders Behring Breivik wanda ya dauki alhakin kashe mutane saba'in da shida a makon da ya gabata, yana da manufar karin wasu hare-hare a zuciyarsa.

Mutane casa'in da shida ne suka mutu a tsibirin Utoeya, sannan takwas kuma suka rasu lokacin da wani bom ya tashi a cikin wata mota a tsakiyar birnin Oslo a wannan rana. Wani kakakin 'yan sanda Paal-Fredrik Hjort Kraby, yace lokacin da ake yiwa Anders Breivik tambayoyi ya tattauna akan manufar wasu hare-haren.

Sai dai kakakin 'yan sandan yaki ya tabbatar da jita-jitar da ake yadawa a kafafen yada labarai cewa daga cikin guraren da Anders ke da nufin kai hari, har da fadar masarautar kasar da kuma cibiyar jam'iyyar Labour.