Ana tattaunawa dangane da batun bashin Amurka

Image caption Barack Obama

Shugaba Barack Obama na Amurka da 'yan jam'iyar adawa ta Republican na tattaunawar gaggawa a Washington don samun mafita game da matsalar bashin kasar da ke neman talauta gwamnatinsa.

Mista Obama ya gana ne da manyan shugabannin 'yan majalisar dokoki na jam'iyar Democrat yayin da kuma ya tattauna ta waya da shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Mitch McConnell.

Fadar gwamnatin Amurkan na bukatar 'yan majalisun ne da su 'dan kara adadin bashin da kasar za ta iya karba zuwa tiriliyan goma sha hudu don baiwa gwamnati damar iya gudanar da harkokin kudi har zuwa bayan zaben da za a yi a badi.

Mista McConnell ya shaidawa manema labarai cewa yana da kwarin gwiwa za a shawo kan matsalar kafin cikar wa'adin ranar Talata.