Mutane 17 sun mutu a siyasar Indonesia

Indonesia sun ce kimanin mutane goma sha bakwai sun rasu sakamakon wani rikicin zabe, a lardin Papua dake gabashin kasar.

Sun rasu ne sakamakon wani rikici tsakanin magoya bayan wasu 'yan takara biyu da ke hamayya da juna, kan zaben da za a gudanar a wani lokaci a cikin wannan shekara.

An cinna wa motoci, da gidaje wuta a wannan rikici, a majalisar dokokin lardin Puncak.