An soki hukunci akan masu tarzoma a Ingila

Barna a lokacin tarzoma a Birtaniya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Barna a lokacin tarzoma a Birtaniya

Wani babban lauya a Birtaniya, Lord Carlile, ya bi sahun jama'ar dake nuna takaici da mamaki, dangane da hukunci mai tsanani da aka yankewa wasu mutanen da ke da hannu a jerin tarzomar da aka yi a Ingila a makon jiya.

Ya ce akwai bukatar hukuncin ya dace da irin laifin da mutum ya aikata.

Masu fafutukar kare hakkin bil'adama sun ce an yanke hukuncin dauri ga jama'a da dama, bisa laifufukan da hukuncinsu gargadi ne kawai.

Hakan dai ya biyo bayan hukuncin daurin shekaru 4 ne da aka yankewa wasu mutane biyu, bisa laifin amfani da dandalin sada zumunta irinsu Facebook ko Twitter, don tunzura jama'a su tada zaune tsaye.

Alhali kuwa a wasu wuraren, irin wannan laifi bai janyowa wadanda suka aikata shi hukuncin dauri.

Sai dai Praminista David Cameron ya sake yabawa kotuna bisa abin da ya kira: tsattsauran sakon da suke aikewa jama'a.