An gano man fetur a Jihar Kwara

man ferur
Image caption man ferur

Gwamnatin jihar Kwara dake arewacin Nigeria ta tabbatar da gano danyen man fetur a karkashin kasa a wani kauye da ake kira Ara -Orin dake a jihar.

Wannan nasara dai za ta iya sanya jihar cikin sahun jihohi a Naijeriya dake samar da man fetur .

Abinda ba a tantance ya zuwa yanzu ba, shine yawan man, da kuma ko ya kai ga sayarwa a duniya.