Majalisar Amurka ta na shirin kada kuri'a kan bashin kasar

'Yan jam'iyyar Democrat da Republican a Amurka na ta ganawa da shugabannin jam'iyyun domin a samu isassun kuri'un goyan bayan kara bashin da Amurka zata iya karba.

Da yake bude zaman majalisar dattawa ranar litinin, shugaban masu rinjiya na majalisar, Harry Reid ya ce ba wanda yake da dukkan abin da ake bukata a shawarar da aka cimma ranar lahadi kan yadda za'a rage bashin.

Ana saran nan gaba a yau duka majalisun dokokin biyu zasu kada kuri'a , gabanin wa'adin kara yawan bashin da Amurka zata iya karba ya cika, na dala triliyon goma sha hudu da biliyan dari uku.