An sasanta game da batun bashin Amurka

Image caption Barack Obama

Shugabannin Jam'iyar Democrat da na Republican da ke Amurka sun cimma yarjejeniya da za ta kara adadin basussukan da kasar za ta iya karba.

Shugaba Obama ne ya sanar da cimma yarjejeniyar kwanaki biyu kafin cikar wa'adin na amincewa da kara yawan basussukan da kasar za ta iya karba.

An cimma yarjejeniyar kara yawan bashin da kasar za ta iya karba ne zuwa fiye da dala biliyan goma sha hudu bayan da 'yan Republican suka dage cewa sai an rage yawan kudaden da ake kashewa da dala biliyan dari tara.

Dole ne dai sai shugabannin majalisun dokokin sun gabatar da yarjejeniyar a zauren Majalisun domin amincewa da ita.