Kamfanin Apple ya fi Amurka kudi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kamfanin Apple ne ke kera wata sumfurin iPad

Kamfanin Apple a yanzu haka yafi gwamnatin Amurka kudin kashewa.

Wasu kididiga na baya-baya nan daga Ofishin Baitul Malin Amurka ya yi nuni da cewa Amurka na da dala biliyan 73.7 ne na kashewa.

Kamfanin Apple kuma ya fito da wasu alkaluma dake nuni da cewa yana da dala biliyan 76.4.

Amurka a yanzu haka na kashe kimanin dala biliyan dari biyu a kowani wata, kuma yawancin kudaden daga kudin shigar kasar ne.

A wani bangaren kuma kamfanin Apple, na kara samu riba ne daga cinikaiyarsa.

A cikin watanni uku, kamafanin ya samu ribar kashi 125 cikin dari, inda kuma ya kashe wajen dalan Amurka biliyan 7.31

Kamfanin na da wajen dala biliyan 75 a bankuna kuma har yanzu dai ba'a san abun da kamfanin zai yi da irin wadannan kudi ba.

Masu sharhi na ganin dai kamfanin na tara kudade ne domin ya sayi wasu fasahohi daga wasu kafanonin domin ya fadada cinikinsa.

Ana dai ganin kamfanin siyarda takardun lataroni na Barnes da Noble da kuma wani shafin nuna fina-finai na Netflix na daga cikin kamfanonin da Apple ke sha'awar siya.

Har wa yau kamafanin ya sa ido, kan kamfanoni dake kera na'urorin kamfuta, kamar wadda ke gane murya wato voice recognition a turance.

A kwanan ne dai kamfanin Apple ya diba daga ajiyarsa inda ya hada gwiwa da kamfanin Microsoft wajen siyan fasahar tsohon kamfanin Canada mai suna Nortel.