Rikicin bashin Amruka: Majalisa zata kada kuri'a

Majalisar dokokin Amruka Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Majalisar dokokin Amruka

Majalisar dokokin Amurka za ta kada kuri'a akan kudirin dokar kara yawan bashin da kasar za ta iya ciyowa.

Majalisar za ta jefa kuria'r ne kafin wa'adin kara yawan bashin da kasar za ta iya karba dake cika a yau.

Shugabannin jam'iyyar Republican da na Democrat sun cimma yarjejeniya a yammacin jiya akan bukatar yin karin.