Za a rantsar da kwamitin sulhu da Boko Haram

jonathan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A lokacin da Shugaba Jonathan ya kai ziyara shalkwatar 'yan sanda bayan fashewar bam

A yau ne shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan zai rantsar da kwamitin da zai tattauna batun sulhu da 'yan kungiyar 'Ahlus Sunnan li Da'arwati wal jihad' wanda ake kira da suna Boko Haram.

Gwamnatin kasar dai tayi tayin afuwa ga 'ya'yan kungiyar idan har suka yarda suka ajiye makamansu, abinda ake gani zai kawo karshe zaman zullumin da ake yi a jihar Borno.

Tunda aka fara tashin hankali tsakanin mahukunta a Najeriya da 'yan kungiyar Boko Haram dai, an tafka hasarar rayuwa da dama da kuma dukiyoyi masu dimbin yawa a yayinda wasu kuma suka jikkata.

Kwamitin da Shugaba Jonathan zai rantsar a yau din da zai kunshi ministoci da mai bashi shawara akan harkokin tsaro.

Amma dai daya daga cikin masu baiwa shugaban kasar shawara akan kyautata dabi'un jama'a Mrs Sarah Jibril ta ce, bisa irin tattaunawar da ta yi da wasu 'yan kungiyar Boko Haram, ta ce akwai alamun za'a sasanta da su.