Majalisar Nijar za ta yi taro kan wani wakilinta a gobe

Majalisar dokokin jamhuriyar Nijar ta yi wani zama na gaggawa a asirce game da koken da wani dan majalisar dokoki na kasa Alhaji Foukori Ibrahim ya kai gabanta.

Hukumomin kasar dai sun hana dan majalisar dokokin barin kasar ba tare da bashi cikkakkiyar hujja ba. Bayan zaman nata majalisar dokokin ta yanke hukuncin gudanar da wata babbar muhawara a kan wannan zance a gobe.

Ta ce za ta gayyato ministan shara'ar kasar malam Morou Amadou domin shi bada haske a game da dalillan da gwamnati ta ke da su na daukar matakin hana wa dan majalisar fita daga kasar.