Venezuela za ta rage cinkoso a gidajen yari

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Venezuela, Hugo Chavez

Kasar Venezuela ta ce tana shirin rage yawan fursunonin da ke gidajen yari a wani yunkuri na rage cunkoso a gidajen yarin kasar.

Sabuwar ministar da ke kula da gidajen yarin kasar Iris Varela, ta ce za a saki fursononi dubu ashirin wadanda suka aikata kananan laifuffuka tare da gindiya musu wasu sharuda.

Ms Varela ta ce fursononin da basu da wata barazana ga jama'a za su kammala wa'adin shari'ar da aka yankewa musu ne a wajen gidan yarin.

An nada Ms Varela ne a matsayin sabuwar minista mai kula da gidajen yari a watan jiya, bayan wani mummunan fada da aka gwabza a gidan yarin El Rodeo wanda ya yi sanadiyar mutuwar fiye da mutane talatin.