BBC ta nemi a saki 'yar jaridarta a Masar

Shaimaa Khalil Hakkin mallakar hoto other
Image caption Shaimaa na daga cikin masu hada shirye-shirye na BBC a Masar

BBC ta yi kira ga mahukuntan kasar Masar da su saki daya daga cikin masu hada shirye-shiryenta da suka kama a kasar.

A ranar Litinin ne 'yan sanda suka kama Shaimaa Khalil a dandalin Tahrir dake birnin Alkahira.

An kamata ne jim kadan bayan da 'yan sanda da sojoji suka tarwatsa masu zanga-zanga da suka shafe makonni uku a can.

Wakilin BBC ya ce kamar yadda masu fafutukar kare hakkin bil adama suka fa di Shimaa na daya daga cikin mutane tamanin da biyun da aka kama ranar Litinin da daddare a dandalin Tahirir, ciki harda 'yan jaridar kasar ta Masar da dama.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce an daki masu zanga-zangar sannan aka fasa wayoyinsu na salula.

Suka kara da cewa an nufi duk wanda ya yi kokarin daukar hoto.

"Mun damu matuka kan tsare Shaimaa Khalil. Kwararriyar 'yar jarida ce, da ke aikinta cikin ruwan sanyi. Muna yin duk abinda ya kamata domin ganin an sake ta," a cewar wata sanarwa da BBC ta fitar.