Majalisar dattawan Amurka ta amince a kara bashi

Shugaba Obama
Image caption Shugaba Obama

Majalisar dattawan Amurka ta kada kuri'ar amincewa da kudirin dokar kara yawan bashin da kasar zata iya ciwowa.

Hakan ya bai wa Shugaba Barrack Obama damar sa hannu akan kudirin dokar ta yadda kasar zata iya biyan bashin da ake binta.

Shugaba Obama dai yayi maraba da amincewar, yana mai cewa shi ne matakin farko, na ganin cewa Amurka ta daina kashe fiye da kudaden da take samu.

Kafin haka majalisar wakilan Amurka ita ma ta kada kuri'ar amincewa da shirin dokar.