Dakarun Syria na tunkarar tsakiyar Hama

Dakarun Syria na tunkarar tsakiyar Hama Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Akalla mutane 140 masu fafutuka suka ce an kashe daga ranar Lahadi

Dakarun kasar Syria na tunkarar tsakiyar birnin Hama a ci gaba da luguden wutar da suke yi a birnin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Mazauna garin sun shaida wa BBC cewa jama'a da yawa sun fice daga garin zuwa kauyukan da ke makwaftaka, suna tsoron cewa sojoji za su kwace iko da garin.

A ranar Litinin, jami'an tsaron sun kaddamar da hare-hare kan masu zanga-zanga a sassan kasar daban-daban, bayan kammala sallah a ranar farko ta azumin watan Ramadan mai alfarma.

Ana saran Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai koma tattaunawa kan batun na Syria.

Kafin yanzu dai Rasha ta ki amincewa da duk wani kuduri da zai yi Allah wadai da rikicin na Syria, amma yanzu ta ce za ta goyi bayan kalamai masu sassauci.

Ministan tsaro na Syria Ali Habib na daga cikin mutane biyar a gwamnatin shugaba Bashar al-Assad, wadanda takunkumin hana tafiye-tafiye na Tarayyar Turai ya shafa.

Kasar Italiya ta kira jakadanta a Syria domin tattaunawa kan abin da ta kira mummunan cin zarafin da ake yi wa jama'a.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun ce akalla mutane 140 aka kashe tun daga ranar Lahadi, yawanci a birnin Hama.

Gwamnatin Syria ta yi alkawarin gudanar da sauye-sauye amma ta ce dakarunta da kuma fararen hula na fuskantar hare-hare daga kungiyoyin masu dauke da makamai da wasu gwamnatocin kasashen waje ke marawa baya.

An hana 'yan jarida na kasashen duniya shiga Syria, don haka yana da wuya a tantance bayanan da shaidu da kungiyoyin masu fafutuka ke bayarwa.