Kasashen duniya na kara sa matsin lamba kan Syria

Masu zanga-zangar na matukar nuna adawa da shugaba Asad Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga-zangar na matukar nuna adawa da shugaba Asad

Ana cigaba da samun dambarwar diplomasiyyar kasa da kasa akan garin Hama dake arewacin Syria.

Tarayyar Turai na kara sawa kasar takunkumi, kuma kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya na tarurruka inda ake sa ran kwamitin zai fitar da wata sanarwa akan Syria.

A daya bangaren kuma, ana cigaba da dauki ba dadi tsakanin masu zanga-zanga da dakarun gwamnati a Hama.

Kasar Italiya ta dawo da jakadanta gida domin nuna rashin jin dadi da yadda rikicin ke gudana a Syria.