Majalisar dinkin duniya ta gana akan Syria

syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zaman dar dar a Syria

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi wani taron gaggawa a sirrance a New York don tattauanawa a kan wani kuduri wanda ya yi Allahwadai da matakan sojin da gwamnatin Syria ke dauka a kan masu zanga-zanga.

Rasha ta ki yarda a amince da kudirin amma ta ce za ta iya amincewa da wanda bai kai shi tsauri ba.

Wani jami'in kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch, Reed Brody, ya yi kira ga kasashen duniya su dauki mataki:

Brody yace"Al'ummar Syria na dandana kudarsu ne saboda abin da ake ganin tsoma bakin da ba shi da iyaka a Libya".

Rasha da China da wasu kasashe masu tasowa sun ce ba za su sake rattaba hannu ba akan tankukumi ba.

Sai dai kuma matsalar ita ce ta hanyar kin daukar mataki suna ba da dama a ci gaba da kisan kiyashi.