An fara shari'ar Hosni Mubarak

An fara shari'ar Hosni Mubarak Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jirgin da ya dauko Hosni Mubarak daga asibiti zuwa kotu

An fara shari'ar tsohon shugaban Masar Hosni Mubarak, wanda aka tilastawa barin mulki sakamakon mummunar zanga-zangar adawa da mulkinsa a watan Fabreru.

An garzaya da Mr Mubarak zuwa kotun wacce ke cibiyar horas da 'yan sanda a gadon daukar marasa lafiya inda masu adawa da shi suka rude da murna.

Ana zarginsa ne da cin hanci da rashawa da kuma bada umarnin kashe masu zanga-zanga - tuhumar da ke daukar hukuncin kisa.

Ya'yansa Alaa da Gamal, da tsohon ministan cikin gida Habib al-Adly da kuma wasu jami'ai shida suma na fuskantar zargin.

Sai dai Hosni Mubarak da 'ya'yan nasa duk sun musanta zargin da ake yi musu.

Akalla sojoji da 'yan sanda 3,000 ne aka girke domin tabbatar da doka da oda a cibiyar horas da 'yan sandan domin shari'ar.

An dai gina wani keji domin wadanda ake zargin kuma ana saran mutane 600 za su kalli zaman kotun.

Rashin tabbas

Mr Mubarak, dan shekaru 83, an kaishi birnin Alkahira ne daga asibitin da yake jinya a tsibirin shakatawa na Sharm el-Sheikh, inda ake tsare da shi tun watan Afrilu.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Hosni Mubarak yana sauraron shari'a a wani keji a cikin kotun

An kuma tura shi zuwa wani daki inda yake sauraron shari'ar tare da sauran wadanda ake zargi ciki harda 'ya'yansa biyu.

Mai shari'a Ahmed Refaat ya bude zaman kotun da neman ayi shiru, yana mai cewa "wayayyun jama'ar Masar na bukatar nutsuwa... Domin ganin kotun ta cimma burinta, don haka za mu godewa Allah madaukakin sarki".

Kowa ya dimauce, a cewar wakilin BBC Jon Leyne, saboda wannan wani lokaci ne wanda babu wani dan kasar Masar - koma a yankin Gabas ta Tsakiya baki daya - da ya yi tunanin gani.

Ba kowa ya amince ba

Tsohon shugaban ya yi murabus ne ranar 11 ga watan Fabreru, bayan an shafe kwanaki 18 ana zanga-zangar adawa da mulkinsa, inda aka kashe kusan mutane 850.

Lauyan Mr Mubarak ya nace cewa tsohon shugaban na fama da mummunar rashin lafiya. Wakilinmu ya ce yawancin jama'ar kasar basu amince da hakan ba.

"Ba na zaton akwai wanda yake da amannar cewa za a yi shari'ar gaske mai cike adalci," a cewar wani mai zanga-zanga Nariman Yousseff.

An samu barkewar tarzoma a wajen kotun tsakanin magoya bayan Mubarak da kuma masu adawa da shi.

A watan da ya gabata jama'a sun kara komawa dandalin Tahrir domin nuna rashin amince da yadda ake jan-kafa kan sauye-sauye da ake yi a kasar.

Daga cikin bukatunsu harda ganin an gaggauta shari'ar da ake yi wa Hosni Mubarak da sauran jami'an gwamnatinsa.

Tuni dai aka yankewa tsohon Ministan cikin gida Mr Adly, hukuncin daurin shekaru 12 a gidan yari kan halarta kudaden haram.

Karin bayani