Amurka ta sassauta akan agaji zuwa Somalia

somaila Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Somalia na fama da matsananciyar yunwa

Gwamnatin Amurka ta sassauta matsayinta akan cibiyoyin bada agaji dake aiki a yankunan Somalia dake karkashin ikon kungiyar nan ta Al Shabbab.

A cewar shugaba Obama cibiyoyin agajin zasu iya bada taimakon abinci a yankunan da Al Shabbab ke iko kuma ba za a hukuntasu ba.

Wakilin BBC Yusuf Garrard ya ce, inda yake nuni da cewar matakin Amurkan tamkar matsin lamba ne ga Al Shabbab don ta daina saka siyasa akan bala'in dake faruwa a yankin.

Kungiyar Al Shabab wacce keda alaka da Al Qaida ce keda iko a wasu yankunan Kudanci da tsakiyar Somalia.

Yankunan da suka hada da Bakool da Shabeelle inda majalisar dinkin duniya ta bayyana cewar ana fama matsananciyar yunwa.

Ita dai majalisar dinkin duniya a baya bayanan ta ce duk wani tallafi da za a kai ba zai shafi 'yan kungiyar Al Shabab ba.

Amma kuma sai gashi Alshabab din na tambayar cibiyoyin bada agaji su biya kudin rijista da kuma haraji akan ma'aikatansu, a yayinda babu tabbas ko Amurka zata amince da wannan abu.

Bugu da kari dai, matakin gwamnatin Amurka na jaddadawa cibiyoyin bada agajin dake aiki a Bakool da Shabeelle da ma duk yankunan dake karkashin ikon Al Shabab cewar kada suji tsoron komai, zai iya zamowa kwarin gwiwa ga sabbin ciboyi su fara kai dauki a yankunan.

Har wa yau matakin zai matsawa Al Shabab ta bude kofofinta ga cibiyoyin agajin, koda yake dai Al Shabab din bata ga maciji da wasu cibiyoyi kuma ta harmatawa wasu daga ciki shiga yankunanta kamar shirin samar da abinci na majalisar dinkin duniya wato WFP wanda suke takun saka na shekaru da dama

Al Shabab ta zargi cibiyar ta majalisar dinkin duniya cewar tana bada abinci kyauta a lokacin girbi abinda kuma ke shafar yadda manoma ke maida hankali wajen ayyukan gona.

Abu na biyu dake daure kai shine cewar Amurka na kallon Al Shabab a matsayin kungiyar 'yan ta'adda kuma duk wanda yayi hudda da ita zai fuskanci fushin Amurkar.

Amma a yanzu tunda Amurka ta yi garan bawul akan matsayarta, tabbas cibiyoyin agaji zasu yi aiki a yankunan Al Shabab ba tare da dari dari ba.

Sai dai babbar tambaya anan itace ko Al Shabab zata sakanka matakin Amurkar, ta hanyar yin lale marhabin ga cibiyoyin dake da niyyar ceto rayukar mata da kananan yara a Somalia.