Dakarun Syria na kara kutsawa birnin Hama

Tankoki ya ki na kutsawa cikin garin Hama Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tankoki ya ki na kutsawa cikin garin Hama

Masu kare hakkin jama'a a birnin Hama na kasar Syria sun ce dakarun Syrian sun kutsa da tankokin yaki zuwa tsakiyar birnin, bayan da suka rika luguden wuta da makaman igwa da kuma bindigogi.

Tun ranar lahadi ake kai farmaki cikin birnin na Hama, bayan da dakarun da suka yi masa kofar-rago suka fara yunkurin dannawa cikinsa, tare da kokarin karbe iko da shi.

Mutane sama da dari ne aka bada rahoton an kashe tun daga lokacin.