An kashe jami'in tsaro a Afghanistan

afghan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Babu zaman lafiya a Afghanistan

An ba da rahoton cewa wani jami'in hukumar 'yan sandan ciki ya rasa ransa sakamakon fashewar wani bom a gefen hanya a lardin Kunduz da ke arewacin Afghanistan.

Jami'ai sun ce yara uku sun jikkata a harin, wanda kungiyar Taliban ta ce ita ta kai shi.

Kwanaki biyu da suka gabata ma an kashe wasu jami'an tsaro masu gadi a wani harin kunar bakin wake a birnin Kunduz.

Kwanan nan dai sojojin sa kai na Afghanistan sun kara kaimi a hare-haren da suke kaiwa kan jami'an leken asiri, da 'yansanda, da jami'an tsaro.