An janye dokar ba motocin sufuri kariya a Agades

Taswirar Jumhuriyar Nijar Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Taswirar Jumhuriyar Nijar

Rahotanni daga jihar Agadez dake Arewacin Jumhuriyar Nijar sun ce hukumomi sun janye dokar nan dake ba sojojin kasar damar bada kariya ga motocin sufuri dake zuwa jihar Agades da wadanda ke tashi daga jihar .

Rahotannin sun ce hukumomi sun dauki matakin ne a jiya, bayan da suka lura cewa yanzu an samu raguwar matsalar fashi da makami a yankin.

A wata hira da BBC, magajin garin Agades, Malam Rhissa Feltou ya tabbatar cewa a jiya ne hukumomi suka dauki wannan mataki, yanai mai cewa yanzu zaman lafiya ya dawo yankin saboda kusan duka jamar yankin dake rike da makamai sun riga sun mika su ga hukumomi ko kuma suna shirin yin hakan.

Tun a shekara ta 2007 ne dai aka kafa wannan doka, sakamakon sake barkewar tawaye a yankin na Arewacin kasar.