Syria na cigaba da fuskantar matsin lamba

asad Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zaman zullimu a Syria

Ana kara matsin lamba a kan Syria tun bayan da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah-wadai da yadda gwamnatin kasar ke amfani da karfi a kan farar hula.

A wata sanarwa da ya fitar bayan rarrabuwar kawuna ta tsawon lokaci, Kwamitin Sulhun ya kuma ce tattaunawar siyasa a karkashin jagorancin al'ummar kasar ce kawai za ta magance rikicin.

Da yake ganawa da manema labarai bayan zaman Kwamitin sulhun, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon, ya ce "bayan doguwar muhawara a kan wannan batu, yanzu dai bakin Kwamitin sulhu ya zo daya da yin Allah-wadai da wannan tashin hankali, da kuma kira ga dukkan bangarori su dau matakan da suka wajaba don kawo karshen rikicin da kuma hawa teburin shawarwari".

Lebanon ce kadai kasar da a kwamitin sulhun da bata goyi bayan matakin na majalisar dinkin duniya ba. Kuma mataimakiyar wakilin dundun dun na kasar a majalisar dinkin duniya Carolin Ziade ta bayyana matsayin kasar.

Ziade tace "duk da cewar muna nuna rashin jin dadinmu saboda kisan mutanen da basu ji ba basu gani ba sannan kuma muna ta'aziya ga iyalansu, da gwamnatin Syria da kasar baki daya, amma kuma Lebanon ta nesanta kanta da wannan sanarwar da aka fitar".

Watanni biyar da suka gabata ne dai aka fara zanga-zangar ta neman sauyi na dimomkuradiyya, kuma an ba da rahotannin ci gaba da ita a sassan da dama na kasar bayan sallar isha'i jiya.

Rahotanni da ba a tabbatar da su ba sun ce tankokin yaki sun shiga tsakiyar birnin Hama yayin da ake barin wuta da rokoki da bindigogi na igwa