Gwamnatin Italiya za ta tsuke bakin aljihunta

Silvio Berlusconi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Silvio Berlusconi

Prime Ministan Italia Silvio Berlusconi ya ce gwamnatinsa za ta gaggauta daukar matakan tsuke bakin aljuhu a wani matsayin yunkuri na baya-bayan nan da ake yi na tinkarar matsalar tattalin arzikin wasu kasashe masu amfani da kudin Euro.

Wannan yunkuri na zuwa mako guda bayan da kasuwannin kudi a duniya ke fuskantar matsala.

Kasar Italia dai na daga cikin kasahen da ake da fargaba akan tattalin arzikinsu a Tarayyar Turai.

Tun farko dai shugaban Amurka Barrack Obama ya yi kokarin tabbatarwa kasuwannin kudi na duniya cewa komai zai lafa.