Italiya da Spain ba za su bukaci tallafiba - Rehn

Kasuwannin hannun jari
Image caption Kasuwannin hannun jari sun fadi a sassa da dama na duniya

Kwamishinan harkokin kudi na Kungiyar Tarayyar Turai, Olli Rehn ya ce duka kasashen Italiya da Spain ba za su bukaci wani tallafi don ceto tattalin arzikinsu ba.

"Babu wata hujja da kasuwannin hada-hadar kudade na duniya za su shiga wani mawuyacin hali saboda fargabar da ake nunawa kan raunin tattalin arzikin wasu kasashen Turai masu amfani da kudin bai daya na Euro.

Babu hujja ta bayyana babbar damuwa dangane da tattalin arzikin Girka," kamar yadda ya shaida wa wani taron manema labarai a Brussel.

Darajar hannayen jari dai ta ci gaba da faduwa a kasuwannin hada-hadar hannayen jari na Asiya da Turai, abun da ya jefa manyan kasuwannin kudi na duniyua cikin wani mawuyacin hali a cikin kwanaki 7 din da suka gabata.

Babban abun da ya sa cikin masu zuba Jari dai ya duri ruwa a yanzu, shi ne yadda suka ga alamun farfadowar tattalin arzikin kasashen duniya, na ja da baya.

A yanzu haka akwai alamun matsalolin basussukan da suka addabi wasu kasashen Turai na neman kara rincabewa, inda ake ganin mai yiwuwa hasashen da ake yi na cewar daya daga cikin kasashen Spain ko Italia ba za ta iya sauke nauyin basussukan da ke kanta ba ya zama gaskiya.

An dan samu kwarin gwiwa

Bankuna a dukkanin wadannan kasashe suna ta tashi-fadin ganin wanda zai iya basu bashi a sakamakon wannan al'amari.

Bugu da kari kuma akwai damuwa kan cewar wannan al'amari yana iya komawa wata sabuwar matsala ta karancin kudi da za ta shafi kasashen Turai baki daya, abun da kuma zai shafi bunkasar tattalin arzikin kasashen Turan.

Alkaluman sabbin ayyukan da aka kirkiro a Amurka a watan Yuli sun dan fara kwantar da hankulan masu zuba jari.

Guraben ayyuka 117,000 ne aka kirkiro - wanda ya haura hasashen da aka yi matuka.

Yawancin ayyukan dai masana'antu masu zaman kansu ne suka samar da su.

Sai dai adadin wadanda basu da ayyukan yi ya tsaya ne a kashi 9 da digo daya cikin dari.

Karin bayani