Karancin ruwan sama a wasu sassan Nijar

Karancin ruwan sama a wasu sassan Nijar
Image caption A baya ma Nijar ta yi fama da matsalar fari

Gwamnatin Nijar ta yi kira ga al'umma da su shirya salloli da addu'o'i na rokon ruwa a ko'ina cikin fadin kasar, bayan da ake fuskantar karancin ruwan a wasu yankuna.

A ranar Asabar ne hukumomin kasar suka shirya gudanar da irin wannan sallar ta rokon Allah ya sauko da rahamarsa a ciki kasar.

Ministan ayyukan noma na kasar Malam Sa'idu Uwa ya sanar da taron majalisar ministocin kasar irin matsalolin da ake fuskanta.

A baya dai jamhuriyar Nijar ta sha fama da matsalar karancin fari wacce ke yin mummunar illa ga amfanin gona.

A wasu lokutan lamrin kankai matsalar yunwa wacce ke yin sanadiyyar mutuwar mutane da dama musamman yara kanana da mata.

Wannan lamari dai na zuwa a daidai lokacin da ake fama da matsalar karancin abinci a kasar Somalia.