Ameachi ya maida martani akan rahoton malalar mai

Rotimi Ameachi
Image caption Gwamnan jihar Ribas Rotimi Ameachi

A Najeriya, ana ci gaba da samun martani dangane da rahoton da Hukumar kula da muhalli ta majalisar Dinkin Duniya ta gabatarwa shugaban kasar, Dr Goodluck Jonathan dangane da tasirin malalar mai a kan al`ummar Ogoni da ke yankin Niger-Delta.

Rahoton ya bayyana cewa rayuwar al`ummar na fuskantar hadari sakamakon gurbacewar muhalli, kuma raya yankin zai bukaci dala miliyon dubu.

Kazalika rahoton ya dora alhakin gurbcewar muhallin a wuyan kamfanoni masu aikin hakar mai da kuma mazauna yankin da ke fasa bututan mai da nufin sata.

Gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi ya bayyana cewar sakamakon rahoton ya wanke mutanen Ogoni kuma ya kamata ayi gyara saboda al'ummar Ogoni a baya sun fuskanci wahala sakamakon bata musu muhalli.