An kama wani jirgin dakon mai a Sudan

Taswirar Sudan ta Kudu Hakkin mallakar hoto wikipidia
Image caption Taswirar Sudan ta Kudu

Gwamnatin Sudan ta tsare wani jirgin ruwa da ya yi lodin mai daga Sudan ta Kudu, tana mai zargin hukumomin sabuwar kasar da rashin biyan kudaden harajin fito.

Wani kakakin gwamnatin Sudan ya ce ana tsare da jirgin a garin Port Sudan..

Kodayake bai bayyana ko nawa ne harajin ba.

Wakiliyar BBC ta ce yanzu Sudan ta Kudu ba ta da zabi, illa ta rika fitar da manta ta Sudan, saboda bat a da iyaka da teku, kuma shirin da akeyi na bi ta tashar jiragen ruwan Kenya zai dauki shekaru kafun a kammala shi.