Ana zargin sojojin Syria da kashe wasu masu zanga-zanga

Wasu masu zanga-zanga a Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu masu zanga-zanga a Syria

Masu fafitika a Syria sun ce dakarun kasar sun hallaka akalla masu zanga- zanga bakwai kusa da Damascus babban birnin kasar.

Sun kuma ce an hallaka daya daga cikin masu zanga- zanga a Birnin Homs, yayinda dubban jama'a a sassan kasar da dama suka yi zanga- zanga bayan sallar juma'a.

Wani hoton bidiyo da aka wallafa a yanar gizo ya nuno jama'a da dama na zanga- zanga a unguwar Bab el sebaa a garin Homs, kodayake da wuya a iya tabbatar da sahihincin hoton bidiyon.