Bom ya tashi a jihar Borno

Gurin da wani bom ya tashi a kwanakin baya a Nijeriya Hakkin mallakar hoto nema
Image caption Gurin da wani bom ya tashi a kwanakin baya a Nijeriya

A jihar Borno ta Nijeriya wani bom ya tashi a Unguwar Kwanar Yobe dake birnin Maiduguri, wanda ya razana jama'a da dama, sai dai babu rahotanni na asarar rayuka.

Yanzu haka dai jama'a a birnin na Maiduguri na zargin jami'an tsaro da dasa wadannan bama-bamai a 'yan kwanakin nan, zargin da rundunar tabbatar da tsaro ta JTF ke musantawa.

Wasu rahotanni daga bisani kuma sun ce jami'an tsaron sun bude wuta a wani gurin raba kayan agaji a Maidugurin inda har akai zargin sun kashe wata yarinya.