Shugabbanin Tarayyar Turai na taro kan magance bashin kasashensu

Shugabar Jamus Angela Merkel Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugabar Jamus Angela Merkel

Shugabannin Tarayyar Turai suna cigaba da yunkurinsu na tunkarar matsalar bashin dake addabar wasu kasashe masu amfani da kudin bai daya na Euro.

Wani wakilin BBC ya ce shugabannin na kokarin cimma matsaya ta bai daya ne kafin kasuwannin hada-hadar kudade su bude a ranar Litinin.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta ce manufarsu, ita ce a awaitar da 'yarjejeniyar da aka cimma a watan jiya kan batu kare makomar kudin Euro.

Sai dai wakilin namu ya ce matsalar ita ce, da dama daga cikin majalisun dokokin kasashe, wadanda su ne za su amince da matakan, ba za su koma zama ba har sai watan gobe. Hakanan kuma, akwai fargabar da ke nunawa dangane da koma baya tattalin arzikin duniya.