Kwace lasisin bankuna ba matsala bane-inji babban bankin Nijeriya

Sanusi Lamido Sanusi, gwamnan babban bankin Nijeriya
Image caption Sanusi Lamido Sanusi, gwamnan babban bankin Nijeriya

Babban bankin Nijeriya ya bayyana cewa babu wani dalili da zai sa jama'a su razana su yi gaggawar debe kudaden su daga bankunan da babban bankin ya kwacewa lasisi a karshen mako. Hakan dai ya biyo bayan wasu rahotanni ne da wasu kafafen yada labarai a Nijeriya suka buga, wadanda ke cewa jama'a na kokarin debe kudadensu daga bankunan da aka kwacewa lasisi.

Kakakin babban bankin, Malam Muhammad Abdullahi ya shaidawa BBC cewa an dauki kwararan matakai domin kare dukiyoyin jama'a.