Malami ya bada fatawar jinkirta buda-baki a kololuwar gine-gine

Image caption Burj Dubai

Wani babban malamin addinin Musulunci a Dubai ya bada fatawar cewa wajibi ne jama'ar dake zaune a kololuwar ginin nan mafi tsayi a duniya, wato Burj Dubai, su yi buda baki, bayan wadanda ke kasan ginin sun sha ruwa. Musulmi dai suna shan ruwa ne idan rana ta fadi, amma saboda ana iya ganin ranar idan ana kololuwar gini, wadanda ke zaune a hawa na fiye da 80, dole ne su jinkirta buda bakinsu da mintina biyu, kuma wadanda ke zaune a hawa na fiye da 150 kuma da mintuna uku. Hakanan, wannan fatawa ta shafi Mjusulmain da ke balaguro a cikin jiragen sama, kuma da ma wadanda ke zaune a kan tsaunika suna shan ruwa, bayan wadanda ke kasa sunbuda baki.