Jam'iyyun siyasa sun kafa sabon kawance a Nijer

Image caption Shugaba Muhammadou Issoufou

A jamhuriyar Niger an kaddamar da wani sabon kawancen jam'iyyun siyasa mai suna MRN, kawancen Farfado da kasar Niger ko kuma Mouvance pour la Renaissance du Niger da faransanci. Kawancen dai, wanda ya kunshi jam'iyyu 33, ya maye gurbin tsohuwar hadakar jamiyyun siyasar CFDR ne, wadda ta goyi bayan shugaban kasar, Alhaji Muhammadou Issoufou hawa kan karagar mulki a zaben da aka yi a bana. Manufar wannan sabon kawance dai, ita ce baiwa mulkin shugaba Muhammadou Issoufou cikakken goyon baya domin taimaka masa wajen biyan bukatun al'umomin kasar ta Nijar .