An killace unguwar Tottenham a London saboda rikici

Rikicin Tottenham Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rikicin Tottenham

Tsakiyar Unguwar Tottenham dake Arewacin London ta cigaba da kasancewa a killace, bayan mummunar taromar da aka yi a daren Asabar. Yanzu haka dai masu bincike na neman shaidu a wurin yayinda 'yan kwana-kwana ke cigaba da yayyafa ruwa a baraguzan gine-ginen da aka kona. Tarzomar dai ta barke ne a karshen wata zanga-zangar nuna adawa da 'yan sanda, bayan da suka bindige wani matashi har lahira a ranar Alhamis din da ta gabata. Dan majalisar dokokin da ke wakiltar yankin, David Lammy, ya ce akwai bukatar saka alamun tambaya game da yadda 'yan sanda suka gudanar da ayyukansu a gabannin barkewar tarzomar. Yan sanda 26 da masu zanga-zanga da dama ne suka samu raunuka a lokacin tashin hankalin.

Yanzu haka kuma an kama mutane fiye da 50 dangane da al'ammarin.