An rantsar da Idris Deby sabon wa'adi

An sake rantsar da Shugaba Idriss Deby Itno na Chadi a karo na hudu na wani sabon wa'adin mulkin shekaru 5 a kasar Chadi. Wannan ya biyo bayan lashe zaben da ya yi ne a watan Afrilun wannan shekara tare da gaggarumin rinjaye. Zaben dai 'yan adawa sun kaurace masa. A shekarar alif dari tara da casa'in ne dai Idriss Deby ya hau kan karagar mulki bayan da kungiyar yan tawayen da ya jagoranta ta hambarar da tsohon Shugaba Hissein Habre daga kan mulki.