Darajar hannayen jari sun kara faduwa

an tafka asara a kasuwanin kudi na duniya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption an tafka asara a kasuwanin kudi na duniya

Darajar hannayen jari a sassan duniya dadama na cigaba da faduwa, yayinda ake fargabar cewa Amurka zata sake fadawa kangin koma-bayan tattalin arziki... da kuma tsoron cewa rikicin bashin turai ka iya kazancewa.

Darajar Hannayen jari a Greece tayi faduwar da ba a taba ganin irinta a shekaru goma sha hudu.

Babbar kasuwar hada hadar hannayen jarin London ma ta gamu da komabaya.

Ana fuskantar wadannan matsaloli ne duk da cewa babban bankin turai ya yi amfani da daruruwan miliyoyin EURO don saye takardun bashin Spain da Italia.