Polio: Gwamnatin Kano za ta dauki mataki akan iyaye

Image caption Gwamnatin jihar kaduna za ta bi gida-gida domin daukan matakai akan iyaye

Duk da gargadin da Gwamnatin jihar Kano tayi na cewa zata hukunta duk iyayen da suka ki bada 'ya'yansu a yi musu allurar rigakafin cutar Polio, har yanzu wasu iyayen sun yi kememen bada 'ya'yan nasu a yi musu allurar.

Rahotanni daga jihar na cewa iyaye da dama a wasu sassan jihar musamman a yankunan karkara sun ki bada yayansu a yi musu allurar a gangamin allurar da aka kammala cikin makon da ya gabata.

Hukumomi na kasar da na sauran sassan duniya sun damu da yadda cutar ta Polio ke neman yiwa kasar kome bayan an kusa ganin bayanta.

Ma'aikatar kula da lafiya a Najeriya ta ce kimanin kashi tamanin na yara da suka kamu da cutar Polio, wadanda ba'a yi mu su allurar rigakafi bane.

Mohammad Zango shugaban kungiyar 'yan jarida masu yaki da cutar Polio a jihar Kaduna, ya shaidawa BBC cewa har yanzu mutane na tirjiya, kuma suna hanawa a yiwa 'yayansu alurar.

Gwamnatin Jihar Kano dai ta ce za ta bi gida-gida domin daukar matakai akan iyayen da suka hana a yiwa 'ya'yansu alurar Polio.