Nafissatou Diallo ne neman Strauss-Khan ya biya ta diyya

Image caption Strauss Khan, tsohon Shugaban Hukumar asusun bada lamuni na duniya

Ma'aikaciyar Otel din nan da ta zargi tsohon Shugaban Hukumar asusun bada lamuni na duniya da yunkurin yi mata fyade ta shigar da kara kotu domin a biya ta diyya.

Nafissatou Diallo na neman kotu ce ta ta sanya Mista Strauss Khan ya biyata diyya, saboda abun da ta kira hari mai tsauri da ya kai mata.

Tuni da Mista Strauss-Kahn ya musanta zargin da ake masa, inda yace Nafissatou ta kista zargin ne domin neman kudi.

Nafissatou Diallo dai ta zargi Mista Dominique Straus Kahn ne da kokarin yi mata fyade da karfin tuwo da keta hakkin ta a matsayin mace.

Ta ce tana nema ne ya biya kudin diyya da ba'a kayyade ba.

Sai dai Lauyan Mista Khan ya zarge ta ne da neman kudi kawai abun da kuma ya sa ta kitsa zargin.

Lauyan Mista kan ya ce zargin da Nafissatou ta yi bashi da tushe.

Tsohon shugaban Asusun Bada lamuni na duniya ya riga ya musanta zargin yiwa Nafissatou Dialo Fyade a dakin Otel a birnin Newyork bayan an gurfanar da shi a gaban kuli'a a watan Mayun daya gabata.

Har yanzu dai masu shigar da kara basu yanke shawarar sake gurfanar da shi a gaban kotu, kan aikata babban laifi, saboda bayanan da Nafissatou ta gabatar mu su akan zargi na cin karo da juna.

Baza'a dai nemi hujoji sosai ba, game da karar da Nafissatou ta shigar saboda bana na babban laifi bane.