Kasuwanin hannayen jari na tangal-tangal

Wani mai hada-hadar hannayen jari Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani mai hada-hadar hannayen jari

Kasuwannin hannayen jari a duniya na cigaba da tangal tangal bayan rage darajar kimar kamar bashin Amurka daga mataki na daya zuwa na biyu da akayi da kuma fargabar cewa matsalar tattalin arzikin turai na cigaba da tabarbarewa.

Babban bankin Turai ya yi amfani da daruruwan miliyoyin EURO a yau litinin don saye takardun bashin kasshen Spain da Italia

Sai dai masu aiko da rohotanni sunce matsalar ba a Spain da Italia kawai ta tsaya ba. Wakilin BBC yace baya ga damuwarda ake nunawa akan kasashen turai masu amfani da kudin EURO, da kuma Spain da Italia, akwai matsalar tattalin azikin Duniya ma baki daya da baya bunkusa cikin sauri.

Hakan tasa kasashe fuskantar matsala wajen tafiyar da harkar tattalin arzikinsu