Za mu kawo karshen tarzoma a Burtaniya - Cameron

London
Image caption An kona motoci da gine-gine da dama a tarzomar

Fira ministan Burtaniya David Cameron ya yi alkawarin kawo karshen tarzomar da ake yi a wasu sassan kasar, inda ya nemi Majalisar kasar da ta dawo aiki ranar Alhamis.

An kira Majalisar Dokoki ta dawo ranar Alhamis domin fuskantar tarzomar da ake yi a Ingila, a cewar Fira minista.

Kwamitin gaggawa na gwamnati Cobra ya gana ranar Talata bayan da tarzomar ta fara yaduwa zuwa wasu biranen kasar.

"Za mu yi duk mai yiwuwa domin maido da doka da oda a kan titunan Burtaniya domin jama'ar da ke bin doka," a cewar David Cameron.

Ya kara da cewa za a girke jami'an 'yan sanda dubu 16,000 a kan titunan birnin London ranar Laraba.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption David Cameron ya yi alkawarin daukar tsauraran matakai

'Za ku gamu da fushin hukuma'

A gefe guda kuma, Scotland Yard sun ce wani mutum dan shekaru 26 da aka harba a lokacin tarzomar a unguwar Croydon ya rasu a asibiti.

Mr Cameron ya ce akalla mutane 450 aka kama dangane da lamarin.

Ya yi Allah wadai da abin da ya kira "sace-sace da barna da kuma fashi".

An soke duk wani hutu da aka baiwa wani ma'aikaci a hukumar 'yan sanda kuma za a kai musu dauki daga sassan tsaro daban-daban.

Ya gaya wa masu tarzomar: "Za ku gamu da fushin hukuma. Idan ma kai tsoho ne kuma ka aikata barna, to ka sani da tsufan naka za ka fuskanci shari'a."

Fira Ministan ya katse hutun da yake yi a Tuscany domin tattaunawa kan tarzomar wacce ta fara ranar Asabar biyo bayan wata zanga-zangar lumana a Tottenham bayan da 'yan sanda suka kashe wani mutum.

Karin bayani