An bude taron koli kan lafiya a Abuja

A Najeriya, a yau ne aka fara wani taro don wayar da kan mahukunta da jami'an kiwon lafiya game da hanyoyin amfani da fasahar zamani wajen kiwon lafiyar al'uma.

Wakilai daga kimanin kasashen Afirka goma sha biyar ne ke halartar taron.

Manufar taron dai ita ce kawo sauyi a wajen inganta kiwon lafiyar al`uma, musamman ma mazauna karkara ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Sai dai mafi yawan al'umomin da ke nahiyar, cikinsu kuwa har da Najeriya na fama da karancin ilmi, da abubuwan more rayuwa, wadanda kan taimaka gaya wajen sarrafa na'urorin zamani.