Tarzoma ta barke a Biu bayan kashe wata mata

Taswirar Najeriya Hakkin mallakar hoto System
Image caption Jihar Borno dai na fama da hare-hare 'yan Boko Haram

Tarzoma ta barke a garin Biu na jihar Borno a Najeriya, bayan da aka zargi sojoji da kashe wata mata, inda aka kona gine-gine, a cewar mazauna garin.

Rahotanni sun nuna cewa tarzomar ta biyo bayan zagna-zangar da aka yi ce kan zargin kame wasu malaman makarantar Islamiyya kan wasu dalilai da ba a sani ba.

An dai saki uku daga cikin malaman, amma biyu na hannu, a cewar wani mazaunin garin.

"Daga nan ne sojoji suka fara harbi a sama domin tarwatsa masu zanga-zangar da suka taru," a cewar Babagana Ali. "Harsashi ya sami wata mata aka. Kuma nan take ta mutu, amma danta mai shekaru biyu ya tsira."

Ya kara da cewa an kuma harbi wata matar a kafa, inda aka garzaya da ita asibiti.

Daga bisani masu zanga-zangar sun cinnawa wani bangare na sakatariyar mulkin karamar hukumar wuta, sannan suka kona wata Majami'a.

Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya a jihar Adamawa - wacce rundunar ta Biu ke karkashinta ya tabbatarwa da BBC afkuwar lamarin, amma ya ce kawo yanzu ba zai ce komaiba.