Jirgin ruwan yaki na China ya soma gwaji a cikin Teku

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Katafaren jirgin ruwan yaki na China

Katafaren jirgin ruwan soja da jiragen sama zasu iya sauka da tashi akansa na farko da China ta mallaka ya soma shawagin gwaji a teku.

Kafar yada labarun gwamnatin Chinan tace, katafaren jirgin ruwan yakin wanda asalinsa na tarayyar Soviet ne ya bar tasharsa dake arewa-maso gabashin Chinan, kuma za'a yi amfani da shi ne wajen bada horo da kuma yin bincike.

Sai dai jirgin na bukatar wasu gyre gyre kafin ya fara aiki gabakidaya kuma zai dauki tsawon lokaci kafin ya fara aiki.

A makon daya gabata ne kasar Japan ta nuna damuwa akan abun data kira gazawar China wurin yin cikaken bayani a'kan manufar sojinta.

Akwai wasu kasashen dake cece-kuce Chinar akan iyakar ruwa a tekun South China Sea