Nato ta kashe fararen hula 85 - Libya

Libya
Image caption Irin hare-hare da Nato ke kaiwa a Libya

Gwamnatin Libya ta zargi dakarun Nato ta kashe daruruwan fararen hula a wani hari da suka kai a wani kauye da ke Yammacin kasar. Libya ta ce Nato ta yi ruwan bama-bamai a Majar, Kudu da birnin Zlitan, ranar Litinin domin baiwa 'yan tawaye damar shiga garin.

Jami'ai suka ce fararen hula 85 ne aka kashe, amma Nato ta ce wani ginin soji ta hara, kuma zai yi wuya a samu mutuwar fararen hula.

Wakilin BBC ya ce ya ga akwatina 30 da gawarwakin mutane a wani asibiti a garin, amma babu tabbas kan ko ta yaya mutanen suka mutu.

'Sojojin haya'

A wata sanarwa, Nato ta tabbatar da kai hari a Kudancin Zlitan ranar Litinin, amma ta nace cewa sojoji ta kaiwa harin.

"Nato ta samu bayanan sirri wadanda ke nuna cewa sojojin Kanar Gaddafi na amfani da tsofaffin gidajen gona don kaddamar da hare-hare a kan al'ummar Libya", a cewar sanarwar.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Gaddafi ya yi watsi da kiran da ake masa na ya yi murabus

Ta kaar da cewa: "Ba mu da wata shaida kan mutuwar fararen hula a yanzu, amma akwai yi wuwar a samu mutuwar sojoji ciki kuwa harda sojojin haya".

Dakarun hadin gwiwa sun fara aiki a Libya ne bayan da kudurin Majalisar Dinkin Duniya ya nemi su kare fararen hula.

Mai magana da yawun gwamnatin Kanal Gaddafi, wanda ya jagoranci 'yan jaridar kasashen waje zuwa wurin, ya ce harin ya kashe fararen hula 85, ciki harda yara 33, mata 32 da kuma maza 20.

"Dakarun Nato ba sa banbance sojoji da yara da kuma tsaffi," Abdulkader al-Hawali, kamar yadda Reuters ya ambato wata dalibar likitanci tana fada.

Wakilin BBC Matthew Price ya ce ya ga kusan akwatina 30 da gawarwakin mutane a wani asibiti, a ziyarar da dakarun gwamnati suka sa masa ido.

Rabin jakar dai aka bude ga manema labarai, a cewarsa, inda gawarwakin samari suka fi yawa, tare da kuma yara biyu da mata biyu.