An shiga dare na hudu da barkewar tarzoma a Ingila

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an kwana-kwana da suka kashe gobarar data tashi

An kwashe dare na hudu ana samun barkewar tarzoma da sace sace a wasu biranen Birtaniya.

Wani kwamadan 'yan sanda Mancester ya ce, dakarunsa sun fuskanci tarzoma a mataki daban daban daga gungun masu aikata muggan laifuka dake da zimmar tada zaune tsaye.

A Birmingham birnin na biyu mafi girma a Birtaniyar ma, matasa sun kaiwa 'yan sanda hari da kwalabe, da duwatsu, kuma sun yi sace-sace a wasu shaguna.

Tuni dai aka kama mutane da dama a yankunan na Midlands.

Sai dai rudnunar 'yan sanda birnin Landan na shan kakkausar suka dangane da yadda ta gaza wajen tunkurar tarzomar da ake yi a birnin da ma wasu sassan Burtaniya.

An dai zargi 'yan sandan da gaza yin katabus, yayin da masu tarzomar ke fasa kantuna, inda suke sace kayayyaki.

'Yan sandan dai sun sha fama da kalubale da dama tun bayan abin kunyar nan na saurare da satar wayar jama'a da ake zargin kamfanin News Corporation International da aikatawa.