Hannayen jari sun sake faduwa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ma'aikata a kasuwar hada hadar zuba hannayen jari ta Australia

Farashin hannayen jari ya sake faduwa a kasuwannin kasashen dake gabas mai nisa, kuma hakan yasa rudani a kasuwannin hannayen jari na duniya.

Farashin hannayen jari a Australia ya fadi da kashi daya da digo da shida a daga farkon bude kasuwa, yayin da kasuwar Nikkei ta Japan ma ta samo da kafar hagu.

Wakilin BBC yace a duk lokacin da kasuwar Wall Street ta Amurka ta samu matsala, kasuwannin hannayen jari na kasashen Asia sukan fuskanci faduwar farashi saboda Amurka babbar abokiyar kasuwanci ce ga kasashen Asia.

Bugu da kari ana cigaba da samun fargaba a kan matsalar bashi ta Turai.