Kamfanin Pfizer ya fara biyan diyya a Kano

Pfizer
Image caption Wasu daga cikin yaran da gwajin na Pfizer ya shafa

Kamfanin harhada magunguna na Pfizer, ya soma biyan diyya ga iyalan da yaransu suka rasu ko suka nakasa a jihar Kano ta Najeriya sakamakon gwajin wani magani.

A shekara ta 1996 ne kamfanin Pfizer ya yi gwajin maganin sankarau na Trovan, a kan wasu yara kimanin dari biyu a Kano, a lokacin wata annobar cutar sankarau.

Sha daya daga cikin yaran Allah ya masu rasuwa, yayin da da yawa kuma suka sami nakasa.

Mutum hudu ne daga cikin daruruwan wadanda akaiwa gwajin aka biya diyyar kawo yanzu, bayan samun sakamakon gwajin DNA da aka yi a kansu.

Jami'ai sun ce sakamakon gwajin ne zai tabbatar da mutanen da abin ya shafa a hakika.

Pfizer ya kwashe shekaru da dama yana cewa, laifin cutar sankarau ce ba na maganin Trovan ba.

To amma daga karshe an cimma yarjajeniya a wajen kotu tare da gwamnatin Kano.

To sai dai tun lokacin, wannan shi ne karo na farko da ake biyan cikakkiyar diyya ga wadanda abun ya shafa.

Wakilin BBC a Kano Yusuf Ibrahim Yakasai, ya ce an dade ana samun korafi da kuma sa-in-sa tsakanin kwamitin da ke da alhakin tantance wadanda abin ya shafa da kuma jama'ar da aka yi wa gwajin.